Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Majalisar Dinkin Duniya Suna Kira Ga Sassa A Rikicin Jos Su Kai Zuciya Nesa


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon,da sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, sun yi kira ga dukkan sassa a rikicin Jos su kai zuciya nesa,inda ranar lahadi aka sami mummunar tarzoma bisa sabanin jinsi. Mr. ban, ya kira hasarar daruruwan rayuka da aka yi, abin “takaici”.

Ya yi kira ga shugabannin siyasa da na addini, suyi aiki tare domin tinkarar ainihin abinda ke haddasa tashe tashen hankula tsakanin Fulani makiyaya wadan da musulmi ne,da kuma kiristoci wadanda manoma ne.

A gefe daya,sakatariya Clinton, ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta tabbatar ta hukunta wadanda suke kitsa tashe tashen hankulan.

Akalla mutane metan ne aka kashe a tashe tashen hankulan,wasu kiyasan na nuna adadin ya kai dari biyar.

Ahalin yanzu sojoji ne suke sintiri kan titunan birnin Jos.

XS
SM
MD
LG