Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aljeriya Ta Cimma Yarjejeniya Da Wasu Kasashen Afirka Shida Wajen Yaki Da Taaddanci


Kasar Algeria tace ta cimma yarjejeniya da wadansu kasashe shida a yankin Sahara da kuma Sahel na hada hannun wajen yaki da ta’addanci a kasashensu.

Wani jami’in kasar Algeria yace an tsaida yarjejeniyar ne a wani taro manyan ministoci daga kasashen Algeria, Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritaniya da kuma Niger da aka gudanar a Algeria,Talata. Wannan ne karon farko da kasashen suka gudanar da taro makamancin haka da nufin shawo kan matsalar ta’addanci.

Ministan harkokin kasashen Afrika da arewacin Afrika na kasar Algeria Abdelkader Messahel, yace kasashen bakwai sun amince da yin wani zama tsakanin jami’an soji da kuma kwararru a fannin dakile ayyukan ta’addanci a kasar Algeria watan gobe.

Washington ta yi na’am da wannan yunkurin na inganta hadin kai da nufin shawo kan ayyukan ta’addanci.

XS
SM
MD
LG