Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Goodluck Jonathan Ya Saukar Da Dukkan Ministoci


Goodluck Jonathan Ya Saukar Da Dukkan Ministoci
Goodluck Jonathan Ya Saukar Da Dukkan Ministoci

<!-- IMAGE -->

Mai rikon mukamin shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, ya saukar da dukkan ministocin kasar daga kan kujerunsu, wata daya da 'yan kwanaki a bayan da aka damka masa ragamar mulkin kasar a sanadin rashin lafiyar shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa.

Gidan telebijin na gwamnatin Nijeriya, NTA, shi ne ya bayar da wannan sanarwa da maraicen laraba, ba tare da yayi karin bayani ba. Daga baya, ministar yada labarai mai barin gado, Dora Akunyili, ta gaskata wannan labari tana mai fadin cewa Mr. Jonathan bai bayyana dalilinsa na yanke wannan shawarar ba.

Akunyili ta ce a yau alhamis za a mika wa manyan sakatarori hakkin gudanar da ma'aikatunsu.

A yanzu gwamanonin jihohin Nijeriya masu karfi da tasirin fada a ji da kuma shugabannin jam'iyyar PDP mai mulkin kasar zasu gabatar da sunayen mutanen da suke son Jonathan ya nada a matsayin sabbin ministoci, wanda shi kuma zai gabatarwa da majalisar dattijan kasar don neman amincewarta.

Rushe majalisar zartaswar da Mr. Jonathan yayi shi ne muhimmin matakin farko da ya dauka tun watan Fabrairu, a lokacin da majalisar dokoki ta ayyana shi a zaman shugaban kasa na riko a yayin da shugaba 'Yar'aduwa yake jinya a kasar Sa'udiyya.

'Yar'aduwa ya koma kasar a bayan jinyar watanni uku, amma rabon da a gan shi a bainar jama'a tun karshen watan Nuwamba. Har yanzu babu tabbas kan halin da shugaba 'Yar'aduwa yake ciki. A watan Nuwamba dai, jami'ai sun ce yana fama da wata mummunar cuta ta kumburin rigar zuciya. Har ila yau, an san shugaban yana fama da mummunan ciwon koda.

XS
SM
MD
LG