Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Bayyana Kudurin Ci Gaba Da Jagorancin Yaki Da Ta'addanci - 2002-01-30


Shugaba Bush na Amirka yayi amfani da jawabin da ya gabatar na halin da kasa ke ciki a jiya, wajen sake jaddada aniyar da ya kudurta na ci gaba da jagorancin yakin da Amirka keyi da ta’addanci.

A jawabin daya gabatar jiya da daddare gaban majalisar dokokin Amirka, wanda aka nuna ta gidajen telebijin, shugaba Bush yace Amirka zata ci gaba da yin tsayin daka a yunkure-yunkuren da take yi na farautowa tare da hukumta ’yan ta’adda, yana mai cewa...

PRESIDENT BUSH: "Our Nation will continue to be steadfast..."

FASSARA: Kasarmu zata ci gaba da nuna hakuri da dagewa wajen bin diddigin manufofi guda biyu: Na daya zamu rufe dukkan sansanonin ’yan ta’adda, mu dagula musu shirye-shirye, sa’annan kuma mu hukumta su. Na biyu kuma tilas mu hana yan ta’adda da gwamnatocin dake bidar muggan makamai ko makaman nukiliya jawowa Amirka da sauran duniya barazana.

Shugaba Bush ya kuma lashi takobin hana gwamnatocin dake neman muggan makamai jawowa wasu barazana. Musamman ya ambaci kasashen Koriya ta Arewa da Iraq da kuma Iran. Haka kuma shugaba Bush yayi kira ga Majalisar dokokin Amirka data yi aiki da shi domin taimakon Amirka shawo kan komada, ko kuma tabarbarewar tattalin arziki kasar. Yayi kira ga wakilan Majalisar dokoki da su amincewa dokar ingiza tattalin arziki kuma su dauki mataki ko matakan rage dogaron da Amirka keyi akan mai daga kasashen waje.

XS
SM
MD
LG