Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karzai Ya ce Manyan Jami'an Gwamnati Ne Suka Kashe Minista - 2002-02-15


Shugaban gwamnatin rikon kwarya a Afghanistan, hamid Karzai, ya ce wasu manyan jami'an gwamnati sun hada baki suka kashe wani minista, bayan da aka samu rahotanni tun da farko cewa maniyyata ne da suka fusata suka kashe shi a filin jirgin saman Kabul.

Cikin daren Jumma'ar nan Mr. Karzai ya ce hada baki aka yi aka kulla makarkashiyar kashe ministan domin wasu dalilai na son kai.

Ministan yada labarai na rikon kwarya, Rahim Makhdoom, ya ce biyu daga cikin wadanda ake nema game da kisan, janar-janar ne na soja. Ya ce gwamnatin riko ta Afghanistan tana neman da a kamo, a mika mata wasu mutanen uku wadanda aka yi imanin cewa sun batar da sawu suka bi mahajjata zuwa Saudi Arabiya.

Ministan zirga-zirgar jiragen sama tare da yawon shakatawa a gwamnatin riko, Abdul Rahman, ya rasu a asibiti, a bayan da aka janyo shi daga cikin jirgi aka lakkada masa duka alhamis da daddare.

Shugaba Karzai ya ce wannan kisa ba ya da wata alaka da maniyyatan Afghanistan, wadandaa suka yi kwana da kwanaki suna zaman jiran a kwashe su zuwa aikin hajji a cikin jiragen da gwamnati tayi musu alkawari. Duk da wannan harin, wasu jirage biyu na mahajjata sun tashi yau Jumma'a da safe daga wannan filin jirgi.

Har ila yau rigima ta barke yau Jumma'a a lokacin wani wasan kwallon kafa na sada zumunci tsakanin wata kungiyar Afghanistan da sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa. Masu gadi sun fatattaki 'yan kallo masu dimbin yawa da suka yi kokarin shiga filin wasan na Kabul karfi da yaji.

An ci gaba da wasa duk da wannan artabu, inda 'yan kiyaye zaman lafiya suka lashe wasan da ci uku da daya.

XS
SM
MD
LG