Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Isa Koriya ta Kudu - 2002-02-19


Shugaba Bush ya isa kasar Koriya ta Kudu inda ya ci karo da zanga-zangar nuna rashin jin dadi da yadda ya ambaci kasar Koriya ta Arewa a jerin kasashen da ya kira "Ginshikan Miyagun Ayyuka," wadanda ya ce su ne ke tallafawa ta’addanci, kuma a lokaci guda, su na kokarin tattarawa kansu makaman kare dangi masu tu’annati.

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi dan rikici da gungun masu zanga-zanga a yau talata a wajen ginin wani sansanin sojojin dake birnin Seoul, inda jirgin shugaba Bush ya sauka bayan tasowar shi daga kasar Japan.

A cikin makon jiya masu zanga-zanga sun sha yin tarurrukan gangami a babban birnin kasar. Sun ce tsokacin da Mr. Bush ya yi na bayyana wasu kasashe a zama ginshikan miyagun ayyuka, ya sa tankiya ta kara yin zafi tsakanin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu.

A gobe laraba idan Allah Ya kai mu, shugaba Bush zai gana da shugaba Kim Dae-Jung na Koriya ta Kudu, sannan kuma zai ziyarci shamakin hana ayyukan soja, wanda ya raba Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu.

XS
SM
MD
LG