Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Ce A Kai Kasuwa - 2002-02-22


Koriya ta Arewa tayi watsi da tayin shugaba Bush na tattaunawa, tana mai bayyana shugaban na Amurka a zaman “dan jaririn da bai san komai ba a harkar siyasa.”

A yau Jumma’a ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ta bada sanarwa, tana zargin Amurka da son canja tsarin siyasar Koriya ta Arewa karfi da yaji. Wannan shi ne martanin farko ga ziyarar da Mr. Bush ya kai zuwa Koriya ta Kudu cikin wannan makon, inda ya sake nanata tayin tattaunawa da Koriya ta Arewa domin warware damuwar da Amurka din ke da ita game da kere-keren makamai da Pyongyang keyi.

A ranar alhamis, Mr. Bush ya roki shugaba Jiang Zemin na China da yayi amfani da tasirin abotarsa da Koriya ta Arewa domin taimakawa wajen farfado da yin shawarwari.

XS
SM
MD
LG