Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mubarak Zai Gayyaci Arafat Da Sharon Domin Su Gana - 2002-03-05


Shugaba Hosni Mubarak na Misra, ya ce zai gayyaci firayim ministan Isra'ila, Shimon Peres, da shugaban Falasdinawa, yasser Arafat, domin su gana da nufin tattauna farfado da shirin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

A cikin hirar da yayi da gidan telebijin na CNN a jiya litinin, Mr. Mubarak ya ce yana fatan shawo kan dukkan sassan da su amince da shawarar da Sa'udiyya ta gabatar a zaman dandali na kara yin tattaunawa.

Yarima Abdullahi mai jiran gadon sarautar Sa'udiyya shi ya gabatar ad wannan shawara wadda a cikinta dukkan kasashen larabawa zasu kulla huldar jakadanci da ta tattalin arziki da Isra'ila idan ta janye daga dukkan yankunan Larabawa da ta mamaye a yakin 1967.

Mr. Mubarak ya ce yana son mutanen biyu su zauna kawai su tattauna da junansu bisa fatar wannan zai canja yanayin da ake fama da shi a yanzu, tare da janyo hankulan 'yan Isra'ila da Falasdinawa.

Wani kakakin Falasdinawa ya ce suna masu yin marhabin da kokarin da Misra keyi, amma kuma ya ce Isra'ila ta dage wajen gurgunta duk wani yunkurin wanzar da zaman lafiya.

Wani kakakin Isra'ila ya ce su ma suna marhabin da kokarin an Misra, amma kuma ya ce Mr. Sharon ba zai gana da Malam Arafat ba, ya kuma nace a kan cewa ba su son ganin shugaban na Falasdinawa yana cika baki kawai, suna son ganin ya dauki matakan kwarai.

Ana sa ran Mr. Mubarak zai bukaci Amurka da ta kara tsoma hannu a yunkurin wanzar ad zaman lafiya idan ya gana nan gaba yau talata da Shugaba Bush.

XS
SM
MD
LG