Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Archbishop Tutu Ya Soki Yadda Afirka ta Kudu Tayi Na'am Da Zaben Zimbabwe - 2002-03-24


Fada Desmond Tutu na Afirka ta Kudu ya soki kasarsa a saboda yadda ta amince da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi kwanakin baya a Zimbabwe.

Archbishop Tutu, wanda ya taba cin kyautar lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya, ya fada a lahadin nan cewa Afirka ta Kudu ta kaskantar da kai da ta bayyana wannan zaben a zaman halaltacce.

Afirka ta Kudu tana daya daga cikin kasashen Afirka kalilan da suka amince da zaben shugaban kasa na ranakun 9 zuwa 11 ga watan Maris a Zimbabwe, wanda ya kara wa'adi ma shugaba Mugabe a kan shekaru 22 da yayi yanzu kan mulki, duk da cewa shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu yana daya daga cikin shugabannin kungiyar "Commonwealth" uku da suka jefa kuri'ar dakatar da Zimbabwe daga cikin wannan kungiya.

Kungiyar ta "Commonwealth" mai wakilai 54 ta kasashen da akasarinsu Ingila ce tayi musu mulkin mallaka, ta dakatar da Zimbabwe a makon da ya shige, tana mai cewa ba a yi wannan zabe tsakani da Allah ba.

Bishop Tutu ya ce yayi bakin cikin cewa Afirka ta Kudu tana daya daga cikin kasashen da zasu fito su ce an gudanar da zaben na Zimbabwe tsakani da Allah.

Fada Tutu ya ce a da, yana mutunta shugaba Robert Mugabe sosai, amma kuma ya ce irin halayyan da yake nunawa a baya-bayan nan ba masu karbuwa ba ne ko kadan.

Gwamnatin Mr. Mugabe ta shata wasu sabbin gonakin turawan da za a kwace a rabawa bakakaen fata marasa galihu, matakin da zai kara fadada shirin da ake gardama a kai, wani lokaci ma har da zub da jini na kwace daruruwan gonakin turawa 'yan kasuwa wanda tsoffin sojojin dake bayyana kansu a zaman 'yan yakin kwatar 'yanci suke aiwatarwa.

XS
SM
MD
LG