Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ce Isra'ila Ta Shirya Amincewa Da Shirin Tsagaita Wuta Na Sasantawa - 2002-03-26


Jaridun Isra'ila, wadanda ke ambatar manyan jami'an kasar, sun ce a bisa dukkan alamu gwamnati zata amince da shirin tsagaita wuta na neman daidaitawa, wanda wakilin Amurka a Gabas ta Tsakiya, Anthony Zinni, ya gabatar.

An ambaci jami'an suna fadin cewa wannan shiri na daidaitawa ya rage wa'adin fara tattaunawar neman zaman lafiya daga lokacin da aka fara yin aiki da shirin tsagaita wuta. Yanzu wannan wa'adi ya komo makonni biyu, daga makonni hudu.

Har ya zuwa cikin daren litinin, jami'an Falasdinawa suna tattauna wannan shawara da Janar Zinni ya gabatar.

A halin da ake ciki, shugabannin Falasdinawa sun ce zuwan Malam Yasser Arafat wurin taron kolin kasashen larabawa da za a yi cikin wannan makon, hakki ne wanda babu wani mahalukin da ya isa ya hana shi.

Tun cikin watan Disamba Isra'ila tayi wa shugaban na Falasdinawa daurin talala a garin Ramallah, ta kuma ce zata kyale shi ne kawai da ya halarci taron kolin idan har an cimma shirin tsagaita wuta.

XS
SM
MD
LG