Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rumsfeld Ya Amince Amurka Ta Horas Da Rundunar Sojojin Afghanistan - 2002-03-26


Sakataren tsaron Amurka, Donald Rumsfeld, ya amince da Amurka ta fara horas da sabuwar rundunar sojoji ta kasa da aka kafa a Afghanistan.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce zaratan sojojin Amurka zasu fara koyawa sojojin Afghanistan muhimman dabarun yaki, da kuma dabaru masu zurfi a cikin makonni hudu zuwa shida.

A halin da ake ciki, jami'an Majalisar Dinkin Duniya, MDD, sun ce sun damu da batun samun kwanciyar hankali a cikin kasar ta Afghanistan, musamman a yankunan dake wajen Kabul, inda babu sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa.

Firayim minista Bulent Ecevit na Turkiyya, ya ce har yanzu ba a cika dukkan sharrudan da zasu sanya Turkiyya ta karbi ragamar jagorancin rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya a Kabul ba.

Turkiyya tana son sauran kasashen su ba ta tabbacin sojoji da kayan aiki, da kuma agajin da zai maida mata da kudi kimanin dala miliyan 60 da take tsammanin kashewa wajen kula da sojojinta na tsawon shekara guda a Afghanistan.

XS
SM
MD
LG