Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya Ya Roki 'Yan Tawayen UNITA - 2002-03-29


Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, yayi kira ga 'yan tawayen UNITA na kasar Angola da su yi na'am da shirin samar da zaman lafiya na gwamnati, wanda aka tsara da nufin kawo karshen yakin basasar shekaru fiye da 26.

Cikin sanarwar da ya bayar a ranar alhamis, Kwamitin Sulhun ya fada ta hannun shugabansa, Jakada Ole Peter Kolby na kasar Norway, cewa kiran da gwamnatin Angola ta yi kwanakin baya na fara tattaunawa da 'yan tawayen UNITA, "mataki ne na ci gaba, kuma na hangen nesa" a kokarin kawo karshen wannan rikici, tare da komawa ga shirin yin sulhu.

Kwamitin Sulhun yayi kira ga kungiyar UNITA da ta yi la'akari sosai da irin wannan dama ta musamman da aka samu ta kawo karshen wannan rikici a cikin mutunci.

Tun shekarar 1975 UNITA take yakar gwamnatin Angola, a lokacin da kasar ta samu 'yancinta daga Portugal, har zuwa watan da ya shige a lokacin da aka kashe madugun kungiyar kuma wanda ya kafa ta, Jonas Savimbi, a wata gwabzawa da sojojin gwamnati.

Jim kadan a bayan, gwamnatin Angola ta ayyana tsagaita bude wuta na radin kanta, aka kuma fara tattaunawa tsakanin sassan biyu a ranar 13 ga watan Maris.

Kwamitin Sulhun ya ce a shirye yake ya nazarci dage takunkumin tafiye-tafiyen da ya kafa a kan jami'an UNITA da iyalansu. Har ila yau ya ce watakila zai bada umurnin bude ofishin MDD a kasar Angola, wanda aka rufe a shekarar 1999.

XS
SM
MD
LG