Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhun MDD Zai Gana Yau Laraba Kan Rikicin Gabas Ta Tsakiya - 2002-04-03


Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, yana shirin ganawa yau laraba domin tattauna rikicin gabas ta tsakiya, yayin da wakilan kasashen larabawa suke ci gaba da matsa lambar cewa lallai a tilastawa Isra'ila tayi aiki da kudurorin da suka nemi dakarunta su janye daga yankunan Falasdinawa.

Wakilan Kwamitin Sulhun sun gana a lokuta dabam-dabam da jakadan Isra'ila a MDD, Yehuda Lancry, da takwaransa na Falasdinawa, Nasser al-Kidwa, jiya talata da maraice.

Malam al-Kidwa ya akwai bukata ga Kwamitin Sulhun da ya bi sawun kudurin da aka zartas ranar asabar, wanda yayi kiran da a tsagaita bude wuta nan take, a kuma janye dukkan sojojin Isra'ila daga garuruwa da biranen Falasdinawa a yankin Yammacin kogin Jordan.

Jakadan Isra'ila a majalisar ya ce gwamnatinsa zata janye sojojinta ne kawai da zarar an cimma tsagaita wuta.

A halin da ake ciki, Isra'ila ta bukaci Babban Sakataren MDD, Kofi Annan, da ya bukaci hukumomin Sham(Syria) da Lebanon da su hana 'yan sari-ka-noken kungiyar Hizbullah girka sojoji da makamai da suke yi a kusa da bakin iyakar Lebanon da Isra'ila.

Shugaban kungiyar Hizbullah, Sheikh Hassan Nasrallah, ya sha nanata kira ga Larabawa da su bada goyon bayansu na baki daya ga Falasdinawa a yakin da suke yi da mamayar da Isra'ila tayi wa kasarsu.

XS
SM
MD
LG