Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karzai Ya Ce Afghanistan Tana Cikin Tsananin Bukatar Agajin Kasashen Duniya - 2002-04-11


Jagoran gwamnatin rikon-kwarya a Afghanistan, Hamid Karzai, ya roki kasashen duniya da su gaggauta mikawa kasarsa dubban miliyoyin dalolin agajin da suka yi alkawari, domin hana kasar sake fadawa cikin fitina.

A lokacin da yake magana jiya laraba a lokacin da aka fara gudanar da wani taron kwanaki biyu a birnin Kabul, an ambaci Mr. Karzai yana fadin cewa Afghanistan tana iya sake fadawa cikin gwagwarmayar neman mulki tsakanin shugabannin sojojin sa kai masu gaba da juna, sai fa idan an gaggauta ba ta karin agaji.

Yayi kashedin cewa zai yi wuya a iya murkushe ta'addanci idan har ba a bai wa Afghanistan damar sake gina kasa ba.

An yi alkawarin bai wa Afghanistan agajin kudi fiye da dala miliyan dubu 4 cikin shekaru biyar masu zuwa, a wajen wani taron kasashen duniya da aka yi a Tokyo cikin watan Janairu.

ya zuwa yanzu, duka-duka abinda aka mikawa Afghanistan bai kai dala miliyan dari uku ba.

XS
SM
MD
LG