Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Bullo Da Sabon Shirin Horas Da Sojojin Afirka - 2002-05-01


Ya zuwa karshen wannan sabon watan na Mayu da muka shiga a yau laraba, jami'an Amurka suna sa ran zasu bada sanarwar sabon shirin horas da sojojin kasashen Afirka, wanda zai maye gurbin Shirin Horas da Sojojin Kare Zaman Lafiya na Afirka, "ACRI" a takaice, wanda aka yi shekaru biyar da kaddamarwa.

Wakilin Muryar Amurka a ma'aikatar tsaro, ya a cikin shekaru biyar da kaddamar da shirin "ACRI," an horas da sojoji fiye da dubu 8 da 600 daga kasashen Afirka dabam-dabam kan dabarun kare zaman lafiya, da gudanar da ayyukan jinkai a lokacin fitina. A yanzu, ana sake garambawul ga wannan shiri da gwamnatin shugaba Clinton ta bulo da shi.

Jami'an ma'aikatar tsaron ta Amurka sun ce koda yake shirin zai ci gaba da inganta kuzarin sojojin kasashen Afirka wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya, haka kuma za a yi wasu 'yan sauye-sauye domin a magance matsaloli da batutuwan da jami'an tsaron kasashen Afirka suka koka da su. Babban jami'in dake kula da harkokin da suka shafi Afirka a ma'aikatar tsaron Amurka, Michael Westphal, yayi bayanin cewa kasashen Afirka suna daukar shirin horaswa da ake kira "ACRI" a zaman wanda ba a iya yi masa sauyi domin la'akari da yanayin wasu wuraren dabam, yana mai cewa: ACT: WESTPHAL: “When it first came out, one of the complaints was that we just kind of put this thing together, rolled it out, and said,........”

VOICE: A lokacin da wannan shiri na ACRI ya fara fitowa, daya daga cikin koke-koken da muka samu shine cewa, mun zauna ne, muka harhada shirin (ba tare da tuntubar kowa ba), muka kuma ce mai son shiga ya shiga, wanda ba ya so kuma shi ke nan. A wannan karon, muna tuntubar kawayenmu a fadin nahiyar Afirka, domin tabbatar da cewa mun ji ta bakinsu, ta yadda zamu tabbatar da abubuwan ad suke ad muhimmanci a gare su, da wadanda ba su da muhimmanci, sannan kuma da wuraren da suka kamata mu fi bada fifiko. END ACT

TEXT: Majiyoyi a Pentagon sun ce maimakon a tsara shiri guda daya tak da za a yi amfani da shi wajen horas da sojoji a duk fadin nahiyar Afirka, kamar yadda ake gudanar da shirin ACRI, yanzu za a tsara shirin da zai dace da kowace kasa ce dabam. Za a tsara shirye-shiryen horaswa ta yadda za a biya muradin wata kasa a wannan fanni, alal misali, kasa guda zata bukaci horaswa kan kula da lafiyar sojojinta a bakin daga, ko girka sojoji ko harbo kayayyakin bukatu daga sama, ko kuma gyara kayayyaki a bakin daga. Duk wadannan za a tsara su a gudanar da su tare kuma da horaswar da aka saba ta kare zaman lafiya da gudanar da ayyukan jinkai. Mr. Westphal ya ce wannan muhimmin sauyin alkibla ne aka samu. ACT: WESTPHAL: “I think we often get caught up on Africa as one place. There are many places, and we...” VOICE: Ina tsammanin a lokuta da dama, mu kan dauki Afirka a zaman wuri, ko kasa, guda kawai. Amma wannan ba haka ba ne. Akwai kasashe dabam-dabam, masu al’adu dabam-dabam a nahiyar Afirka. Saboda haka, bai kamata mu tsara shiri guda bisa zaton cewa zai yi aiki a kowace kasa ta nahiyar ba. Kamata yayi mu nazarci rundunar sojan kowace kasa dabam, mu ga wuraren da ta fi karfi, da inda take neman gyara, mu nazarci irin abubuwan da zamu iya yi wajen magance inda ta nuna kasawa. END ACT

TEXT: Jami'an ma'aikatar tsaro suna tattaunawa da hukumomi daga kasashen Afirka dabam-dabam da kungiyoyi ko hukumomi na yankunan nahiyar dabam-dabam, ciki har da kasashen da tuni har sojojinsu sun samu horaswa a karkashin shirin farko na ACRI, da kuma wadanda suke da kwarewa wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya.

Majiyoyin ma'aikatar tsaro ta Pentagon suka ce akasarin kasashen na Afirka sun yi marhabin da wannan sabon shirin. Amma suka ce jami'an Afirka sun gabatar da takamammun shawarwari, ciki har da wani sabon fasali na horaswar da ake gudanarwa kan kare hakkin bil Adama a cikin shirin farko na ACRI. Wannan sabon fasalin horaswa zai jaddada dabarun yin shawarwari da na kula da gungun jama'a masu zanga-zanga ko makamantansu.

Jami'an Pentagon suna daukar wannan sabon shiri a zaman na dindindin, ba wai na takaitaccen lokaci kamar shirin farko na ACRI ba.

A bayan samun shawarwari daga kasashen Afirka ma, ma'aikatar tsaron ta Amurka tana kokarin neman goyon bayan kasashen Turai kamar su Ingila, Faransa, Jamus da Portugal. Makasudin neman goyon bayan shine domin a tsara irin taimakon soja, ko na tsaro, da kasashen Turai suke bai wa kasashen Afirka, da shirin horaswar na Amurka, ta yadda za a fi cin moriyarsu baki daya.

XS
SM
MD
LG