Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Shirye-Shiryen Karshe Na Fara Wasan Cin kofin Kwallon Kafa Na Duniya - 2002-05-15


Saudi Arabiya ta doke Senegal da ci 3-2, a wani wasan sada zumuncin da shine na karshe da kowaccensu ta buga kafin wasan cin kofin kwallon kafar duniya da za a yi a Japan da Koriya ta Kudu.

Wani bugu daga wajen yadi na 18 da Hassan al-Yami ya buga wa 'yan Sa'udiyya, ta kuma fada cikin raga ana minti na 15 da komowa daga hutun rabin lokaci, ya zamo shine sinadarin lashe wannan wasa ga kasar ta larabawa. Kyaftin na 'yan Sa'udiyya mai suna Sami al-Jaber, wanda aka fi sani da sunan "Dila sarkin Wayo" shi ya fara jefa kwallo a raga a bugun daga kai sai mai tsaron gida, ko fenariti, a minti na 8 da fara wasa.

Souleymane Camara ya ramawa 'yan Senegal wannan ci, ana dab da tafiya hutun rabin lokaci. Amma kuma ana komowa daga hutun, sai Ibrahim al-Suwaid na Sa'udiyya ya harba kwallo guda cikin raga. Minti biyu kacal bayan wannan, sai Senegal ta sake ramowa lokacin da El Hadj Diouf yayi bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Saudi Arabiya, wanda wannan shine karo na uku ad take zuwa gasar cin kofin duniyar, zata gwabza a rukuni na biyar, ko "E", tare da Jamus da Ireland da kuma Kamaru.

Senegal, wanda wannan shine karon farko da take zuwa gasar, tana rukunin farko, ko "A", tare da Faransa, wadda ke rike da kofin a yanzu, da Uruguay da kuma Denmark.

A yau laraba dukkan kungiyoyin biyu zasu tashi zuwa Koriya ta Kudu. A karshen wannan wata za a fara gasar cin kofin kwallon kafar ta duniya a Koriya ta Kudu da Japan.

XS
SM
MD
LG