Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yau Litinin Majalisar Loya Jirga Zata Sake Kokarin Zabar Tsarin Majalisar Dokoki... - 2002-06-17


Babbar majalisar shawarwarin kasar Afghanistan ta Loya Jirga, ta yi shirin sake taruwa a yau litinin, bayan da aka yi kwana guda ana tafka zazzafar muhawara game da fasalin majalisar dokokin rikon kwarya.

Shugaban kasar Afghanistan, Hamid Karzai, zai yi jawabi ga 'yan majalisar ta Loya Jirga, a wani kokarin samar da wata jituwa tsakankanin wakilan dake halartar taron, wadanda ke fama da rarrabuwar kai a sanadiyyar bambancin kabila.

Shugaban babbar majalisar shawarwarin, ya kawo karshen muhawarar jiya lahadi, lokacin da mahalarta babban taron suka kasa zaben ko daya daga cikin wasu tsare-tsaren fasali biyu masu goggaya da juna.

Wakilan lardunan da suka fi yawan mutane su na so a ba su wakilci daidai da yawan mutanen lardunansu, wato a zabi dan majalisar dokoki daya ya wakilci yankunan wakilai 10 na majalisar Loya Jirga.

Amma wakilan kabilar Pashtun sun goyi bayan wani shirin da yayi tanadin wakilai bibbiyu ga kowace guda daga cikin lardunan Afghanistan su 32, ba tare da yin la'akari da yawan jama'arsu ba.

XS
SM
MD
LG