Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wace Kasa Ce Tayi kaurin Suna Wajen Zarmiya Da Cin Hanci? - 2002-08-28


wata kungiyar yaki da zarmiya da cin hanci a duniya ta ce wannan matsala ta zamo ruwan dare a kusan kashi 70 daga cikin 100 na kasashen da ta bincike su.

Kungiyar "Transparency International" mai hedkwata a birnin Berlin ta gabatar da rahotonta mai auna yawan zarmiya da cin hanci, inda ta gwada gwamnatocin kasashe 102 a duniya, ta kuma bai wa kowacce maki daga 1 zuwa goma. Wadda ta samu goma ita ce ba ta nuna zarmiya da cin hanci, yayin da mai maki daya kuma tayi kaurin suna.

Kungiyar ta ce saba'in daga cikin wadannan kasashe da ta auna ba su samu makin da ya kai biyar ba.

Kasar Finland ita ce ta daya a fadin duniya wajen rashin zarmiya da cin hanci, inda ta samu maki 9 da digo 7.

Kasar Bangladesh a wannan karon ita ce ta fi nuna alamun cin hancin da zarmiya, inda ta samu maki daya tak da digo 2.

Britaniya ita ce ta 10 a duniya wajen nuna gaskiya, yayin da Amurka take ta 16.

XS
SM
MD
LG