Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Australiya, Da Afirka Ta Kudu Da Nijeriya Suna Ganawa A Abuja - 2002-09-23


Shugabannin Australiya da Nijeriya da Afirka ta Kudu suna ganawa a Abuja, babban birnin Nijeriya, domin tattauna takunkumin da kungiyar Kwamnwels ta sanyawa kasar Zimbabwe.

Wannan kwamitin kasashe mai suna "Troika" wanda kasar Britaniya da kasashe 53 da ta yi wa mulkin mallaka suka kafa tayi fatan bayyana damuwarta kai tsaye ga shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe. Amma kuma sai ya ki yarda ya halarci wannan taro na Abuja a yau litinin. Jami'an Zimbabwe sun bayyana wannan taro a zaman na yaudara kawai.

An dakatar da kasar Zimbabwe daga halartar tarurrukan diflomasiyya na kungiyar Kwamanwels na shekara guda, a bayan da kungiyar ta ce zaben shugaban kasar da aka yi cikin watan Maris bai bayyana ainihin muradun al'ummar Zimbabwe ba.

'Yan adawar kasar sun ce har yanzu suna fuskantar danniya da tashin hankali. haka kuma, har yanzu ana ci gaba da kokarin fatattakar turawa daga cikin gonakinsu, duk da karancin abincin da ake fama da shi a Zimbabwe.

XS
SM
MD
LG