Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Biyar Suka Mutu A Harin Bam A Philippines - 2002-10-17


Mutane biyar sun mutu, yayin da wasu akalla 144 suka ji rauni lokacin da bama-bamai biyu suka tashi a birnin Zamboanga dake kudancin Philippines. Hukumomi sun ce dukkan bama-baman biyu sun tashi cikin mintoci 30.

Magajiyar garin birnin na Zamboanga tayi kira ga hukumomi a birnin Manila da kuma rundunar sojoji da su karfafa matakan tsaro a birnin.

Wakiliyar Muryar Amurka, Katherine Maria, ta aiko da rahoton cewa 'yan sanda da sojoji suna kokarin tattara bayanai game da hare-haren bam din da aka kai kan wasu manyan kantuna biyu da tsakar rana a birnin Zamboanga. An yi amfani da motocin daukar marasa lafiya da na 'yan sanda da kuma motocin a-kori-kura wajen jigilar wadanda suka ji rauni daga wurin. Asibitocin da sauran cibiyoyin kula da lafiyar jama'a suna kokarin kula da dimbin mutanen dake bayyana da rauni.

Roilo Golez shine mai bai wa gwamnatin kasar shawara a kan harkokin tsaron kasa. ACT: GOLEZ: "Right now we cannot pinpoint anyone who is responsible for this act. We, at the national..."

FASSARA: A yanzu dai ba zamu iya cewar ga wanda ya aikata wannan abu ba. Hukumomin tsaron tarayya suna nazarin wannan lamari sosai. Da ma tun bayan harin bam na Bali (a kasar Indonesiya) muke zaune cikin shirin ko ta kwana. (FAKAT)

Kwanaki biyar da suka shige, mutane kusan 200 sun mutu, wasu daruruwan mutanen kuma sun ji rauni a wani harin bam a tsibirin Bali na Indonesiya. Akasarin wadanda suka sheka barzahu, 'yan kasashen waje ne masu yawon shakatawa. Babu wata alamar cewa hare-haren na Zamboanga suna da wata alaka da harin bam na Bali.

'Yan sanda a kudancin Philippines suna yin tambayoyi wa mutane fiye da 10 dangane da hare-haren na Zamboanga. Wasu daga cikinsu kuwa, 'yan kasashen waje ne.

Zamboanga birni ne da akasarin mazaunansa kiristoci ne 'yan darikar Roman Katolika, kuma yana yankin da akasarin mutanensa Musulmi ne. Akwai kungiyoyi da dama a yankin cikinsu har da kungiyar Abu Sayyaf mai zazzafan ra'ayi wadda Amurka ta ce tana da alaka da kungiyar ta'addanci ta al-Qa'ida.

Magajiyar garin birnin na Zamboanga, Maria Clara Lobregat, ta ja kunnen jama'a da su yi taka tsantsan saboda yiwuwar karin hare-haren ta'addanci, tana mai fatan za a karfafa matakan tsaro a filayen jiragen sama da tasoshin jiragen ruwan birnin. ACT: LOBREGAT: "I hope I can get more support from the military, from our government for them to..."

FASSARA: Ina fatan samun karin taimako daga rundunar sojoji da kuma gwamnatin tarayya, kuma ina fata zasu fahimci cewa ya zamo wajibi a dauki wani mataki nagari a wannan yanki na kasa. (FAKAT)

Makonni uku da suka shige, wani bam ya tashi kusa da wani gidan barasa a Zamboanga ya kashe sojan Amurka daya da wasu 'yan kasar ta Philippines su uku. 'Yan sanda sun dora laifin wancan harin a kan kungiyar Abu Sayyaf.

XS
SM
MD
LG