Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 13 Sun Mutu, 40 Sun Ji Rauni A Fashewar Bam A Isra'ila - 2002-10-21


Wani bam ya fashe a kusa da wata motar safa a yankin arewacin Bani Isra'ila, ya kashe mutane akalla 13 tare da raunata wasu 40 a harin da aka bayyana a zaman na kunar-bakin-wake da maraicen litinin din nan.

Rahotanni sun ce wata karamar motar da aka cika da nakiya, ta tarwatse a kusa da wannan motar safa, wadda ke jigila a tsakiyar lokacin da jama'a ke tashi daga aiki a kusa da garin Hadera dake bakin teku.

Kungiyar kishin Falasdinu ta "Islamic Jihad" ta dauki alhakin kai wannan harin.

Shugabannin Isra'ila sun dora laifin harin a kan shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, wanda ya yi tur da harin.

Shi ma shugaba Bush yayi tur da harin, yana mai cewa tilas ne a nemi hanyar cimma zaman lafiya, kuma tilas a kawo karshen tashin hankali.

Tun da fari, rundunar sojojin Isra'ila ta ce dakarunta sun harbe Falasdinawa biyu suka kashe su, a lokacin wani dauki-ba-dadin da aka yi da bindigogi a kusa da unguwar yahudawa 'yan kama-wuri-zauna da ake kira Kfar darom a zirin Gaza.

XS
SM
MD
LG