Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Britaniya Suna Fuskantar Wuta Mai Tsanani A Basra - 2003-03-25


Sojojin Britaniya sun bayyana birnin Basra dake kudancin Iraqi a zaman sansanin sojan da zasu iya kaiwa farmaki, a bayan da suka fuskanci wuta mai tsanani daga sojojin gwamnati da fararen hula sojan sa kai.

Ba a san ko sojojin Britaniya dake kewaye da Basra suna shirin shiga birnin ko kuma a'a ba.

Wani wakilin Muryar Amurka ya ce koda yake tun kwanaki da dama da suka shige sojojin taron dangi suka shiga kudancin Iraqi, har yanzu suna fuskantar wuta mai tsanani daga sojojin sa kai na Iraqi.

Sai dai kuma ba sojojin sa kai masu yakin sari-ka-noke ne kawai suka addabi sojojin na Britaniya ba. Su ma sojojin gwamnati da na igwa masu biyayya ga shugaba Saddam Hussein suna bude musu wuta.

Wani kakakin sojojin Britaniya ya ce duk wani soja ko jami'in gwamnatin dake wannan birni na biyu wajen girma a Iraqi ya zamo abinda za a iya kaiwa hari. Sai dai kuma bai ce ko sojojin Britaniya suna shirin shiga birnin ba.

Sojojin taron dangi dai suna kokarin kaucewa shiga tare da gwabzawa a cikin birane har sai bayan sun karya lagon sojojin Iraqi.

A halin da ake ciki, sojojin taron dangi suna farauta domin ceto wasu sojojin Britaniya guda biyu wadanda suka bace ranar lahadi a bayan da aka yi kwanton bauna aka far ma kwambar motocinsu.

A yau talata, jami'an Britaniya sun bada sanarwar cewa an kashe sojojin Britaniya biyu a kudancin Iraqi, sojojin kasar na farko da aka kashe a bakin daga tun fara yaki kwanaki shida da suka shige.

XS
SM
MD
LG