Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata Shugaba Charles Taylor Na Liberiya Yayi Murabus... - 2003-05-19


Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, ya ce ya kamata shugaba Charles Taylor na Liberiya yayi murabus domin kare lafiyar dukkan 'yan Afirka ta yamma.

Ruud Lubbers yayi wannan furuci a karshen ziyarar mako guda a yankin na Afirka ta yamma. Yayi zargin cewa shugaba Taylor shine barazana mafi muni ga kwanciyar hankali a duk Afirka ta yamma. Har ila yau yayi kiran da a tura rundunar kiyaye zaman lafiya zuwa Liberiya, kasar da akasarin yankunanta ke hannun 'yan tawaye masu adawa da Mr. Taylor.

Gidan rediyon Liberiya ya ce Mr. Taylor zai gana da shugabannin 'yan tawayen Liberiya domin tattaunawar neman zaman lafiya cikin wata mai zuwa a kasar Ghana.

A farkon watan nan MDD ta sakle sabunta takunkumi kan Mr. Taylor bisa hujjar cewa yana ingiza wutar yake-yaken basasa a Afirka ta yamma ta hanyar safarar makamai da duwatsun lu'ulu'u da katako. Masu gabatar da kararraki na kasa da kasa kuma sun ce ya bada mafaka ga mutanen da ake zargi da laifin cin zarafin bil Adama a lokacin yakin basasar Saliyo.

XS
SM
MD
LG