Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Rwanda Sun Bayyana Goyon Baya Mai Karfi Ga Sabon Tsarin Mulki - 2003-05-27


Sakamakon farko da ake samu daga kuri'ar raba-gardamar da aka gudanar kan sabon daftarin tsarin mulki a kasar Rwanda ya nuna cewa masu jefa kuri'a sun amince da gyare-gyaren da aka yi wa tsarin mulkin da gagarumin rinjaye.

A yayin da aka kidaya kusan rabin kuri'un da aka kada, jami'an zabe sun ce kimanin kashi 90 daga cikin 100 na masu jefa kuri'a sun yi na'am da daftarin tsarin mulkin.

Sabon tsarin mulkin zai yi kokarin aza harsashin dimokuradiyya da kwanciyar hankali a wannan kasa, kusan shekaru 10 a bayan da gwamnatin tsageranci ta 'yan kabilar Hutu masu rinjaye ta kitsa kisan kiyashin da aka yi wa mutane kusan dubu 800, tsiraru 'yan kabilar Tutsi da ma 'yan kabilar ta Hutu masu sassaucin ra'ayi.

XS
SM
MD
LG