Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Duniya Sun Bi Sahun Amurkawa Wajen Tunawa Da 11 Ga Watan Satumba - 2003-09-12


Shugabannin duniay sun bi sahun Amurkawa wajen tunawa da mutanen da suka mutu a hare-haren ta'addanci na 11 ga watan Satumba.

Babban sakatatren MDD, Kofi Annan, ya shaidawa Kamfanin Telebijin na Reuters cewa ya kamata cikar shekaru biyu da wadannan hare-hare su tunatar da duniya cewa hada kai yana da matukar muhimmanci ga yakin da ake yi da ta'addanci.

Waziri Gerhard Schroeder na Jamus yayi kiran da a yi hattara a yakin da ake yi da ta'addanci a duniya. A lokacin da yake magana a Frankfurt, wazirin na Jamus ya ce za a iya cin nasarar yakin ne kawai idan kasashen duniya suka gaggauta sake gina kasar Afghanistan.

A Moscow, ministan harkokin wajen Rasha, Igor Ivanov, ya ce kasarsa tana taya Amurka jimamin wannan lamari. Amma kuma yayi kira ga Amurka da ta nemi daidaitawa da kawayenta, furucin da ake jin cewa shagube ne game da yakin da Amurka ta jagoranci kaiwa kan kasar Iraqi, matakin da Rasha ta yi nuna adawarta da shi.

Firayim ministan Australiya, John Howard, ya shiga cikin bukukuwan da aka yi a birnin Canberra, ya kuma lashi takobin cewa kasarsa zata ci gaba da tsoma hannu a yakin da ake yi da ta'addanci.

A birnin London kuma, gimbiya Anne ta bude wani sabon lambun tunawa da wadanda suka mutu a wajen ofishin jakadancin Amurka. Sai dai kuma a wani gefen, wata kungiyar Musulmi ta Britaniya da ake kira al-Muhajiroun ta yaba da hare-haren ta bayyana wadanda suka kai harin a zaman wadanda suka yi shahada.

A halin da ake ciki, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta umurci dukkan cibiyoyinta a fadin duniya da su yi hattara a saboda yiwuwar cewa kungiyar al-Qa'ida zata kai hare-haren ta'addanci kan cibiyoyin na Amurka a kasashen waje.

Ma'aikatar ta ce ta yi imanin za a iya kai sabbin hare-hare kan cibiyoyin Amurka a Turai da bangaren Asiya mai makwabtaka da Turai, watakila a daidai wannan lokaci da ake bukukuwan cikar shekaru 2 da hare-haren 11 ga watan Satumba.

Jami'ai suka ce ba su yanke kaunar cewa al-Qa'ida zata yi kokarin kai wani mummunan harin a nan cikin Amurka ba.

A halin da ake ciki, shugaba Bush ya ce jami'an leken asirin Amurka suna ci gaba da nazarin sabon faifan bidiyo da aka ce na Osama bin Laden ne tare da mukaddashinsa.

Mr. Bush ya ce wannan faifai yana tunawa Amurka cewa har yanzu ana ci gaba da yaki da ta'addanci.

XS
SM
MD
LG