Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbe Aka Kashe Wani Bafaranshe Dan Jarida A Kasar Ivory Coast - 2003-10-22


Wani jami'in tsaro na kasar Ivory Coast ya bindige ya kashe wani Bafaranshe dan jarida mai aiki wa gidan rediyon nan na birnin Paris da ake kira "Radio France International" mai watsa shirye-shirye ga kasashen duniya.

Shaidu sun ce an bindige Jean Helene, wakilin gidan rediyon an RFI a kofar hedkwatar 'yan sanda a Abidjan, cibiyar kasuwanci ta kasar Ivory Coast.

Mr. Helene yana jira ne yayi hira da 'yan ta-kifen adawa su 11 da aka sako.

Mr. Helene, mai shekaru 50 da haihuwa ya fara bayar da labarin bacewar 'yan adawar a farkon makon nan, kuma tun shekarar 1990 yake aiki da gidan rediyon RFI.

Shugaba Jacques Chirac na Faransa ya bayyana kisan Mr. Helene a zaman kisan gilla. Shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast yayi alkawarin gudanar da cikakken bincike.

Magoya bayan gwamnatin Ivory Coast suna zargin 'yan jaridun kasashen waje da laifin nuna fifiko ga 'yan tawaye dake rike da arewacin kasar.

XS
SM
MD
LG