Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Kungiyar 'Yan Tawayen Liberiya Ta Janye Barazanar Ficewa Daga Cikin Gwamnati - 2003-10-29


Babbar kungiyar 'yan tawayen Liberiya ta janye barazanar da ta yi ta janyewa daga cikin gwamnati, a bayan da aka cimma daidaiton ra'ayi da sabon shugaban rikon kwarya na kasar.

Kakakin majalisar dokoki, kuma babban jami'in 'yan tawaye George Dweh, ya ce an cimma yarjejeniya da maraicen litinin a bayan da shugaban rikon kwarya, Gyude Bryant,ya ce zai sake duba sunayen mutanen da 'yan tawaye suka zaba domin a ba su manyan mukaman gwamnati.

A makon da ya shige, Mr. Bryant ya ki yarda da sunayen mutane uku da 'yan tawayen kungiyar LURD suka gabatar domin a ba su manyan mukamai a gwamnatin ta rikon kwarya.

Mr. Brynat ya ce yarjejeniyar zaman lafiya ta baya bayan da aka cimma ba ta ware mukaman domin 'yan tawaye ba. Amma 'yan tawaye sun zargi Mr. Bryant da laifin keta yarjejeniyar.

'Yan tawayen kungiyar ta LURD sun bukaci Mr. Bryant da yayi murabus. Sun yi kashedin cewa idan har ya ki, to zasu fice daga cikin gwamnatin, za su kuma janye alkawarin da suka yi na ajiye makamansu.

XS
SM
MD
LG