Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Harkokin Cikin Gidan Sa'udiyya Ya Musanta Labarin Kama Wasu Mutane Dangane Da Harin Bam - 2003-11-12


Ministan harkokin cikin gida na Sa'udiyya ya musanta rahotannin dake cewa kasar ta kama wasu mutanen da take zaton suna da hannu a harin bam na ranar asabar wanda ya kashe mutane 17 a birnin Riyadh.

Yarima Nayef ibn Abdul-Aziz ya ce har yanzu babu ko ad mutum guda da aka kama, a yayin da hukumomi suke ci gaba da binciken wannan harin da aka kai kan gidajen kwanan jama'a a babban birnin an Sa'udiyya.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ce wata mujallar larabawa mai suna "al-Majalla" da ake bugawa a London, ta samu waya daga wani mutumin da ya ce wai shi dan al-Qa'ida ne yana daukar alhakin kai harin.

Sarki Fahd an Sa'udiyya dai yayi alkawarin murkushe 'yan ta-kife.

XS
SM
MD
LG