Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nada sabon sakataren kasashen wajen Amurka na jan hankalin gabas-ta-tsakiya - 2004-11-16


Ajiye aiki na sakataren harkokin wajen Amurka, Collin Powell da kuma rahotannin maye shi da mai ba shugaba Bush shawara kan tsaro, Condoleezza Rice na jan hankali a gabas-ta-tsakiya. Ajiye aikin Powell bai ba da mamaki ba duk da cewa akwai wadanda suka dauka cewa zai ci gaba da rike mukaminsa. An dauka cewa maye marigayi Arafat da mai sassaucin ra’yi zai sa ya ci gaba a gwamnatin Bush kamar yadda ya yi wasu maganganu a kai.

‘’Ina ganin cewa an samu wata dama a gabas-ta-tsakiya kuma shugaba Bush ya yi magana kan wannan kuma nan da wasu makwanni zan ga irin damar da ake da ita a gabas-ta-tsakiya bayan mutuwar Arafat’’ ,in ji Powell. Ministan harkokin kasashen wajen Isra’ila, Silvan Shalom wanda ya gana da Mista Powell a Washington jim kadan bayan sanarwar ajiye aikin ya ce bai ji dadin ajiye aikin ba. Ya kira shi kyakkyawan abokin Isra’ila kuma mai son samar da zaman lafiya. Ajiye aikin ba a sa ran zai kawo wani babban sauyi kan manufofin kasashen wajen Amurka kan Isra’ila ko kuma tsakiyar gabas-ta-tsakiya.

Tsohon jakadan Isra’ila a Washington, Zalmon Shoval ya ce shi baya ganin Powell a matsayin mai goyon bayan Palasdinu kamar yadda wasu masu kushe shi su ke ganinsa. A maimakon haka ya ce ra’ayinsa kan gabas ta tsakiya kamar na sauran masu goyon bayan larabawa ne a ma’aikatar harkokin waje wanda bai sa ya zama wani cikakken abokin Palasdinawa ba.’’ Ina ga cewa a fili take a cikin zuciyarsa cewa Arafat ba amfanu bane ga Palasdinawa domin ya jawo musu matsaloli wanda yanzu dole ne Palasdinawa su yi gyara’’ in ji Mista Shoval. Mista Shoval ya ce maganar shugaba Bush ta kwanan baya kan gabas ta tsakiya ya nuna irin ra’ayin Isra’ila. Wato Palasdinawa su kafa dimukuradiyya sannan su rusa abinda ya kira cibiyoyin ‘yan ta’adda. Mahdi Abdul Hadi darekta ne na cibiyar nazari kan harkokin duniya ta Palasdinawa shi ma ba ya tsammanin wani sabon abu ko wani sabon yanayi kan samar da zaman lafiya har sai idan Washington ta sauya manufofinta . Mista Abdel Hadi ya ce babu wani shiri na dawo da samar da zaman lafiya a yanzu kuma ba za a samu ba har sai Washington ta kasance tana sauraron sauran kasashen turai.

‘’Condoleeza Rice za ta gane cewa Katanga da ake ginawa cin zali ne kuma dole a tsaya da gina matsugunai kuma dole a saki wadanda ake tsare da su’’ ya ce. ‘’Sauya yanayin dangantaka tsakanin Palasdinu da Isra’ila dole ya zama hakkin Isra’ila da farko ba tare da wasu sharudda ba’’. Kodayake ba a tsammanin wani sauyi ko wani babban kokari na dawo da samar da zaman lafiya an samu labari mai dadi cewa ranar litinin kungiyar Islamic Jihad da kuma ta Al Aqsa sun bayar da sanarwar dakatar da kai hare-hare kan Isra’ila na kwana sittin don samun damar zaben sabon shugaban kungiyar Palasdinawa.

XS
SM
MD
LG