Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan jaridun kasashen yammaci sunce sojojin Iraqi dana Amirka basu gano wadanda akace anyi garkuwa... - 2005-04-18


Yan jaridun kasashen yammaci sunce sojojin Iraqi dana Amirka basu gano wadanda akace anyi garkuwa dasu a birnin Madaen ba, inda hukumomi suka cewa ana garkuwa da mutane kari. A jiya lahadi sojojin kawance na taron dangi suka yiwa birnin dawanya bayan da gidan talibijin na Iraq ya bada rahotanin cewa ’Yan Sunni sunyi barazanar kashe wadanda suke garkuwa dasu cikin sa’o’i ashirin da hudu sai fa idan ’yan Shiya mazauna birnin sun fice.

To amma dan jaridar dake yiwa kamfanin dilancin labarun Faransa aiki ya bada rahoton cewa sojojin Amirka sunce masu ceto sun iske titunan birnin fayau babu kowa, kuma kantuna a rufe a yau litinin.

Wani dan jaridar mai daukarwa kamfanin dilancin labarun Associated Press hotuna, shima ya bada rahoton cewa ba’a samu ’yan tawaye ko wadanda aka ce anyi garkuwa dasu ba. Mazauna birnin da masu lura da harkokin yankin sunce da alama an kara gishiri wajen yayata rahotanin cewa anyi garkuwa da wasu da kila a saboda gaɓar dake tsakanin bangarorin birnin.

XS
SM
MD
LG