Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe yayi bikin cika shekaru ashirin da biyar... - 2005-04-18


Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe yayi bikin cika shekaru ashirin da biyar da kasarsa ta samu ’yanci yana fadawa kasashen yammaci cewa baya bukatar taimakonsu ko kuma yayi amfani da salon manufofin mulkin democradiyarsu.

Shugaban ya fadawa dubban mutane da suka halara a Harare baban birnin kasar a yau litinin cewa yanzu Zimbabwe tana neman sabbin ƙawaye ne daga yankin Asiya, tana juyawa kasashen yammaci baya. Yace zaben da aka gudanar a Zimbabwe a kwanan nan baya bukatar amincewar Amirka ko wata kasar yammacin duniya. Jam’iyar ZANU PF ta Mugabe wadda take jan ragamar mulkin ƙasar ita ce ta samu gagarumar nasarar a zaben wakilan Majalisar dokoki da aka yi a watan jiya.

To amma jam’iyar masu hamaiya da gwamnitocin kasashen yammaci ciki harda Britaniya da Amirka sunce ba’a gudanar da zaben cikin ’yanci da walwala ba. Shugabanin kasashen Afrika da dama ciki harda na jamhuriyar Congo da Tanzania da Angola da kuma Mozambique sun halarci bikin. Tun dai lokacinda Zimbabwe ta samu ’yancinta daga Britaniya shugaba Mugabe ke jan ragamar mulkin kasar.

XS
SM
MD
LG