Lauyoyin ‘yan hamayya a Zimbabwe sunce babbar kotun kasar zata dakata har zuwa Talata kamin ta yanke humunci kan kokarin ‘yan hamayya na tilasta a saki sakamakon zaben shugaban kasa.
Da yake magana da manema labaru litinin,lauyan ‘yan hamayya Alec Muchadehama,yace kotun ta amince tana da hurumin sauraron karar,amma ta jinkirta yanke hukunci kan batun da kwana daya.Jam’iyyar masu hamayya ta MDC tana neman a saki sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi kwanaki tara da suka wuce.