Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Tana Zargin Israila Da Laifin Kashe Wani Kwamandanta


Ana sa ran Alhamis din nan ce jakadan Isra’ila a Ingila zai gana da jami’an Britaniya,domin tattaunawa kan jebun fasfo da wadan da ake zargi dakashe wani kwamandan Falasdinawa na kungiyar Hamas.

Ma’aikatar harkokin wajen Ingila ce ranar laraba ta gayyaci jakadan na Isra’ila Ron Posnor. ‘Yan kasar Isra’ila bakwai,wadanda har wayau ‘yan Ingila ne,sunyi zargin cewa an saci bayanansu aka saka kan fasfunan mutanen da ake zargi da kashe kwamandan Hamas Mahmoud al-Mabhouh.

Cikin watan jiya ne aka kashe shi awani O’tel a Dubai. Hamas tana zargin Isra’ila da aiwatar kisan gillan.

Ranar laraba dubban magoya bayan Hamas ne suka yi gangami a zirin Gaza tareda alwashin zasu dauki fansa kan Isra’ila domin kisan Mabhouh.

Amma ministan harkokin wajen Isra’ila Avigdor Lieberman ya fada jiya laraba cewa babu wani dalili da zai saa zaci hukumar leken asirita kasar Mossad ita ked a alhakin kashe Mabhouh.

XS
SM
MD
LG