Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawaye A Kwango Sun Sake Kwace Wasu Sabbin Yankuna,A Dai Dai Lokacinda Shugabansu,Lauren Nkunda Ya Gana Da Manzon Majalisar Dinkin Duniya,Janar Obasanjo.


Mayaƙan ’yan tawayen jumhuriyar Kongo sun sake ƙwace wasu sabbin yankunan dake gabashi, duk da ƙoƙarin Majalisar Dinkin Duniya keyi na haɗa sassan dake rikici da juna a teburin shawara domin kawo zaman lafiya.

Shaidun gani da ido sun bada labarin cewar mayaƙan ’yan tawayen dake ƙarƙashin jagorancin Janar Laurent Nkunda yanzu suke mamaye da yankin Rwindi mai tazarar kilomita 125 Arewa da birnin Goma cibiyar lardin Kivu dake Arewaci.

An sami wasu rahotannin dake cewa sabon faɗan ya rutsa da sojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, a musayar wuta tsakanin sojin Nkunda da na Gwamnati jiya lahadi, harma an jikkata sojin Majalisar Dinkin Duniya, ɗan ƙasar Indiya guda.

A jiya lahadi, jagoran ’yan tawaye Nkunda ya gana da jakadan MƊD na musamman kuma tsohon shugaban Nigeria Olusegun Oabsanjo, inda ya shaidawa Obasanjo cewar zai yi aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta idan har za’a amince a maida mayaƙan tawayensa cikin runudnar sojin Gwamnatin Congo.

XS
SM
MD
LG