Ƙungiyar tarayyar turai tayi kukan cewar ƙasashen turai goma sha biyar dake amfani da takardun kuɗi na euro na fuskantar matsalar koma bayan tattalin arziki, a dai dai lokacin da shugabannin ƙasa da ƙasa ke haɗuwa a nan birnin Washington DC domin tattauna matsalar da tsarin tattalin arzikin ƙasashen duniya ke fuskanta da hanyar warware matsalar.
Ƙungiyar Tarayyar turai tace an sami koma baya sosai a ƙasashen dajke amfani da euro da kashi biyu daga cikin goma na hada-hadar da aka saba yi a sulusin shekarar nan, saboda koma bayan da ake samu a harkokin cinikayya da durƙushewar kasuwannin hannayen jari.
Ita ma Hong Kong ta bada sanarwar faɗawa cikin layin masu fuskantar talauchi a tsarin tattalin arzikinta. A halin da ake ciki, an kammala shirye-shiryen karɓar baƙuncin shugabannin ƙasashen turan a fadar shugaban Amurka ta White House inda shugaba Bush zai masu tarba ta alfarma a daren yau. A gobe Asabar dce za’a fara taron ƙolin.