Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yar Aduwa Ya Bijirewa AFRICOM


Shugaba Umar Musa ‘Yar Aduwa na Najeriya, yace ba zai kyale ayi amfani da kasarsa ba, wajen kafa sansanin rundunar hadin guiwar Amurka da Kasashen Afirka.

Da yammacin jiya Litinin Shugaban ya baiyana wannan matsayi, bayan ya fito daga taron Majalisar Tuntuba ta Kasa, wacce ta hada da gwamnoni, tsofaffin shugabannin kasa, da wasu fitattun ‘yan siyasar kasar.

Shugaba ‘Yar Aduwa ya kuma ce ba zai goyi bayan kafa wannan sansani ba a ko wacce kasa ta Afirka ta Yamma. A halin yanzu dai cibiyar wannan runduna da ake kira AFRICOM, tana garin Stuttgart na kasar jamus.

Liberiya ce kadai kasar Africa da ta amince ta karbi bakuncin wannan runduna.

Amurka tace AFRICOM zata taimaka wa kasashen Africa su tunkari manyan laifuka, bala’o’i da sauran matsalolin da ka iya barazana ga zaman lafiyarsu.

Amma kasashe da dama, cikinsu kuwa har da Libya da Afirka ta Kudu, sun baiyana damuwarsu cewa wannan runduna zata kara tsananta tasirin Amurka a nahiyar.

XS
SM
MD
LG