Shugaban Amurka Barack Obama yayi jagorancin addu’o’i na musamman da tarukan tunawa da marigayi jagoran masu rajin maras galihun Amurka marigayi Martin Luther King Junior. Yau ltinin ranar hutu ce a nan Amurka domin tunawa da marigayin.
Shugaba Barack Obama yayi jawabi a wata mujami’ar dake kusa da fadar shugaban Amurka ta White house.Mujami’ar da marigayi Martin Luther King yayi wa’azi shekaru hamsin da suka gabata, shugaba Barack Obama ya tuna baya a jawabin marigayin inda yake cewa, yanzu muna samun amfanin abinda marigayin Luther king ya shuka ne, sannu a hankali maras sa galihun Amurka sun fara samun galihun, suna samun ‘yancinsu na walwala kamar kowa.
Wannan ba karamin ci gaba bane aka samu a Amurka. Ana ganin yadda bakar fatar Amurka ke shiga sahun gaba wajen ayyukan ginin kasa, har ta kai Amerkawa sun zabi bakar fatar Amurka shugaban Amurka na 44.