Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kasar Haiti Mutane 800,000 Ne Ke Dauke Da Kolera


Wata Yar kasar Haiti mai dauke da kolera
Wata Yar kasar Haiti mai dauke da kolera

Wani masani mai zaman kansa dake wa MDD aiki ya bayyana jin takaicin ganin cewa MDD din taki daukan alhaki, a shari’ance, na masifar cutar Kolera da ta barke a kasar Haiti, inda ta kama mutane 800,000, har ta hallaka fiyeda 9,300 daga cikinsu.

Philip Alston, wanda masani ne gameda fannonin talauci da hakkokin Bil Adama, yace wannan matsayin na MDD “abin kunya” ne.

A rahoton da ya aikawa MDD din, Alston yace idan har ita kanta majalisar ba zata sa kai, ta dauki alhakkin wannan bala’in ba, bai kamata ta rinka matsawa wasu kasashe daukar nauyin taka hakkokin bil adama da ake a cikin kasashen nasu.

Ana dai zargin cewa cutar ta kolera ta bazu a kasar Haiti ne a sanadin sharer da sojojin kiyaye sulhu na MDD na kasar Nepal suka zuba ne a cikin koguna da gulaben Haiti.

Har yanzu ma ance kowane mako, mutane 500 ke kamuwa da cutar Kolera din a kasar.

XS
SM
MD
LG