Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ADAMAWA: Akwai Takaddama Akan Belin Bala Ngillari Tsohon Gwamnan Jihar


ADAMAWA: Tsohon gwamnan Adamawa ya samu beli
ADAMAWA: Tsohon gwamnan Adamawa ya samu beli

Makonni ukku da suka gabata babban kotun jihar Adamawa ta yanke hukumcin daureshi shekaru biyar amma jiya sai ta bashi beli domin ya nemi magani saboda wai yana da hawan jini da cutar ciwon sukari

Ana ci gaba da sa’insa kan belin da mai shara’a Nathan Musa, alkalin alkalan Adamawa ya baiwa tsohon gwamnan jihar Barrister Bala James Ngillari wanda ya yi zaman katso na kwanaki ashirin da daya daga wa’adin shekaru biyarda shi alkalin alkalan ya yanke masa.

Mai Magana a madadin lauyoyan dake kare tsohon gwamnan Sam Ologunorisa, Barrister Obed Wadzani ya fadawa taron manema labarai a cibiyar ‘yan jaridu ta Yola cewa kaifin hujjojin da suka gabatar gaban kotu sune kotun ta duba ta bada belinsa ba takardar da hukumar gidan yarin Yola ta rubuta ta gabatar gaban shara’a ba.

A daya bangaren kuma, kwamishanan shara’a na jihar Adamawa Barrister Silas Sanga ya ce suna kalubalanta sahihancin takardar saboda suna da takardar da kwana daya bayan kotu ta bada belinsa shugabancin gidan kason ya shaida a rubuce cewa tsohon gwamnan yana cikin koshin lafiya.

A jam’iyyance inji shugaban PDP na jihar Adamawa Barrister Abdulrahaman Bobboi da alamun ana ma ‘ya’yanta bita-da-kulli saboda kawo yanzu ‘ya’yan jam’iyyar uku na zaman katso.

Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG