Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Kotu Ta Ci Tarar Gidan Radiyo da Telibijan Gotel Mallakar Atiku Abubakar


Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasa kuma wanda ya mallaki gidan rediyo da telibijan Gotel dake Yola fadar gwamnatin Adamawa
Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasa kuma wanda ya mallaki gidan rediyo da telibijan Gotel dake Yola fadar gwamnatin Adamawa

Bayan an kwashe shekaru shida da Kabiru Arayu ya shigar da kara yana neman gidan Rediyo da Telibijan Gotel mallakar Alhaji Atiku Abubakar a biyashi hakinsa, yau kotu ta yanke hukunci inda ta tabbatar masa da abun da ya nema.

Babban kotun jihar Adamawa ta yanke hukumcin gidan radiyo da talabijan na Gotel mallakar tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar da ke Yola fadar jihar, ya biya tsohon ma'aikacinsa dan jarida Kabiru Arayu diyyar Naira miljyan shida da dubu dari daya na karar da ya shigar na ci-da-guminsa.

Da ta ke yanke hukunci, mai shari'a Helen Nuhu Hammanjoda ta ce kotu ta dauki wannan matsayin saboda kin biyan dan jaridan hakkinsa na aikin kwangilar da yayi da kotu ta ce ya sabawa sashi na 167 karamin sashi na daya na dokar kasa.

Wannan hukunci na kotu na zuwa a lokacin da kungiyar 'yan jarida ta Najeriya ke kokawa da ci-da-gumin 'ya'yanta inda kafofin yada labarai da jaridu ke daukan 'van jarida ba tare da biyansu albashi ko alawus-alawus ba.

Wasu 'yan jarida da Muryar Amurka tayi hira dasu kan yadda shari'ar ta kaya Husseini Hammangabdo na jaridar Leadership da tsohon shugaban wakilan jaridun Najeriya reshen jihar Adamawa Umar Dankano sun ce shari'ar ta bude wata kafa da 'yan jarida za su kwatar ma kansu hakkinsu.

Yayin da lauya mai kare dan jaridan Barrister Francis Ngaro ke sambarka da yadda shari'ar ta kaya, lauya mai kare gidan radiyo da telabijan na Gotel Ibrahim Gwary ya ce suna duba yiwuwar daukaka karar.

Tun farko, dan jarida Kabiru Arayu ya shigar da kara yana neman diyyar naira miliyan ashirin da tara kamin hukunci da kotu ta bayar na a biya shi naira miliyan shida da dubu daya a shari'ar da ta dau tsawon sama da shekaru biyar.

A saurari karin bayani daga rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG