Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al’amarin Ganganci Da Rashin Tausayi Ne-In Ji Korea Ta Kudu


Gwamnatin Koriya ta Kudu tace ta yarda da cewa Koriya ta Arewa ita ta shirya yadda aka kashe Kim Jong Nam, wanda yake dan uwane ga Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un.

Mai Magana da yawun Ministan Hadaka Jeong Joon-hee yayi wannan batune a yau Lahadi a wani takaitaccen bayani da ya biyo bayan jawabin jami’an 'yan sandar kasar Malaysia da sanyin safiya.

Jeong ya kira al’amarin da “Ganganci da rashin tausayi kuma laifi ne na rashin imani da kuma ta’addanci” wanda Pyongyang ta aikata a baya domin cusa Seoul da sauraran kasashen duniya.

Da safiyar yau lahadi ne dai Yan sandan Malaysiya suka ce suna neman wasu mutane hudu ko fiye da haka yan kasar Koriya ta Arewa wadanda ake zargi, sun bar kasar a ranar da Dan uwan shugaban Koriya ta Arewa ya hallaka a Filin jirgin saman Kuala Lumpur.

Mataimakin Shugaban Yan sanda na kasa Noor Rashid Ibrahim ya bayyana duka mutanen hudu a taron manema labarai a yau Lahadi a Kual Lumpur.

An dai tsare wasu mutane guda hudu, ciki har mata biyu, saurayin daya daga cikin matan da kuma dan Koriya ta Arewa.

Kafin rasuwarsa dai Kim ya fadawa mai akatan lafiya a filin jirgin sama cewar an fesa masa wani abu a fuska da sinadari, yayin da ya fara jin jiri, sai kuma farfadiya ta kamashi inda yam utu cikin kankanin lokaci cewar jami’an Malaysia.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG