Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkali Ya Bayar Da Belin Bukola Saraki Da Mataimakinsa


Bukola Saraki
Bukola Saraki

Babbar kotun tarayya karkashin Alkali Yusufu Halluru, ta tura shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu da tsohon jami’in gudanarwa na majalisar Salisu Mai Kasuwa da kuma wani mutum ‘daya zaman wakafi a gidan Yari.

Sai dai kuma nan take kotu ta bayar da belin su, bisa ka’idar mai tsaya musu ya zamanto yana da gida a unguwar masu kudi dake Sokoro ko Maitama.

Rashin samar da mai tsaya musu kan wannan shari’a ta zargin yin dokokin majalisa na jabu zai sa a turasu gidan Yari dake Kuje.

Joseph Daudu shine lawyan dake kare Bukola Saraki, yace sun roki kotu a jawabinsu da lawyoyi suka saba yi kuma kotu ta amince ta bayar da belinsu. A nasa bangaren lawyan dake kare gwamnati Muhammad Sa’idu ya dage kan kar a baiwa su Bukola beli, amma hakan bai samu karbuwa ba.

Alkalin yace ya bada belin Bukola Saraki da mataimakinsa saboda ba a riga an samesu da laifi ba, kuma wadannan mutane da gwamnatin tarayya ta shigar da kara a kansu suna da kima a idanun duniya, domin mukaman da suke rike da su.

Dinbin magoya bayan Bukola saraki sunyi dafifi a kotun, kotun dai ta dage sauraron karan har zuwa sha ‘daya ga watan Yuli mai zuwa.

Saurari rahotan Madina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:32 0:00

XS
SM
MD
LG