Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta Auna Hari Akan Shugaban Al-Shabab


Mayakan sakai na kungiyar al-Shabab
Mayakan sakai na kungiyar al-Shabab

Amurka tayi anfani da jiragen dake tuka kansu ta kai hari akan ayarin motocin Ahmed Abdi Godane shugaban kungiyar al-Shabab dake Somalia

Jami’ai a ma’aikatar tsaron Amurka (Pentagon) suna kokarin su tantance ko harin da Amurka ta kai da jiragen yakinta da basu da matuka a Somalia, sunyi nasarar kashe shugaban kungiyar mayakan sakai ta al-shabab, Ahmed Abdi Godane.

Kakakin ma’aikatar Rear Admiral John Kirby ya gayawa taron manema labarai cewa Amurka tayi amfani da jiragen yakinta masu matuka da wadanda basu da matuka wajen kai harin da aka auna kan manyan shugabannin kungiyar al-shabab, musamman shugaban kungiyar Ahmad Abdi Aw Muhammad, wand a kuma ake kira Ahmed Godane, a lokacinda suke haramar gudanar da wani garo a yankin saheblle dake kasar.

Rear Admiral Kirby, yace zuwa yanzu basu da cikakken bayani kan sakamakon harin. Duk da haka yace idan har an sami nasarar kashe Godane, hakan zaiyi matukar illa ga illahirin kungiyar, wadda zai shafi karfinsu na ci gaba da kai hare haren ta’addanci.

Shaidu suka ce jiragen da basu da matuka sun kai hari kan wasu motoci uku da suke tafiya kan wata hanya, biyu daga cikinsu makamai masu linzami masu yawa sun afka musu, amma mota ta ukun ta tsere.

XS
SM
MD
LG