Biden ya bayyana hakan ne a taron tsaro da aka ta yanar gizo a Munich, wanda shi ne karo na farko da Biden ke halartar da shugabannin kasashen duniya bakwai da suka fi karfin tattalin arziki a duniya.
“A yau ina mai sanar da cewa Amurka za ta ba da tallafin dala biliyan biyu ga shirin COVAX, da kuma karin wata dala biliyan biyu, don mu kwadaitar da sauran kasashe su ma su kawo ta su gudunmowa.” In ji Biden.
Kokarin shirin na COVAX shi ne a samar da dadaidaito a wajen samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 yayin da kasashe masu arziki ke kokarin tara tulin alluran
Burin shirin shi ne ya samar da allurar biliyan biyu ga kasashe 92 marasa galihu nan da zuwa karshen shekarar 2021.