Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bai Wa Nijar Tallafin Jirgin Saman Soja Samfarin C 120 Don Karfafa Yaki Da Ta’addanci

Amurka Ta Baiwa Nijar Tallafin Jirgin Saman Soja Samfarin C 120 Don Karfafa Yaki Da Ta’addanci
Amurka Ta Baiwa Nijar Tallafin Jirgin Saman Soja Samfarin C 120 Don Karfafa Yaki Da Ta’addanci

Kasar Amurka ta bai wa jamhuriyar Nijar tallafin jirgin sama samfarin C 130 domin karfafa gwiwa ga sojojin kasar a yakin  da suke kafsawa da ‘yan ta’addan yankin Sahel.

NIAMEY, NIGER - Wannan wani yunkuri ne da ke kara jaddada huldar ayyukan soja da ke tsakanin kasashen biyu masu manufa daya akan batun yaki da ta’addanci.

Amurka Ta Baiwa Nijar Tallafin Jirgin Saman Soja Samfarin C 120 Don Karfafa Yaki Da Ta’addanci
Amurka Ta Baiwa Nijar Tallafin Jirgin Saman Soja Samfarin C 120 Don Karfafa Yaki Da Ta’addanci

A yayin wani bukin da ya gudana a filin jirgin saman soja Escadrille da ke birnin Yamai ne mukaddashin Jakadan Amurka Susane N’garnim ta damka wa hukumomin tsaron Nijar wannan jirgi samfarin Cargo C 130 domin amfanin sojojin kasar wadanda aka yi amannar cewa suna taka rawa sosai a yakin da ake gwabzawa da kungiyoyin ta’addancin yankin Sahel.

Jami’ar hulda da ‘yan jarida a ofishin jakadancin Amurka a Nijar Aichatou Ambarka ta yi mana magana akan wannan tallafi.

Ministan tsaro Alkassoum Indatou ya yi godiya a madadin gwamnatin Nijar da ma al’ummar kasar baki daya, domin a cewarsa wannan gudunmawa ta gwamnatin Amurka babban alheri ne da ke kara wa kasar ta Nijar karfin soja.

Amurka Ta Baiwa Nijar Tallafin Jirgin Saman Soja Samfarin C 120 Don Karfafa Yaki Da Ta’addanci
Amurka Ta Baiwa Nijar Tallafin Jirgin Saman Soja Samfarin C 120 Don Karfafa Yaki Da Ta’addanci

Ya ce samun wannan tallafi na jirgin C 130 abu ne da ke saka rundunar mayakan Nijar a sahun wadanda suka fi takwarorinsu wadatattu kuma ingantattun kayan aikin jigilar soja a kasashen da ke yankin kudancin Sahara. Muna godiya ga Amurka da wannan gudunmowa.

Amurka na kan gaba a jerin kasashen da suke yi wa Jamhuriyar Nijar rakiya a fannonin da suka shafi sha’anin tsaro banda maganar kayan ayyukan soja da Nijar din ke samu irinsu motocin yaki da na’urorin zamani.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Amurka Ta Baiwa Nijar Tallafin Jirgin Saman Soja Samfarin C 120 Don Karfafa Yaki Da Ta’addanci.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00

XS
SM
MD
LG