Kasar dake yankin tsakiyar Afrika ta ce kodayake an sake bude hada-hadar kasuwanci da Najeriya saboda saukin hare-haren ‘yan boko haram da aka samu cikin shekaru 2 da suka gabata, duk dan kasuwar da zai je Najeriya ya koma kasar dole ne sai anyi mai binciken kwakwaf.
Daruruwan ‘yan kasuwa sun koma kasuwar Lami dake kan iyaka a yankin jihar arewa mai nisa dake kasar kamaru. Sun cigaba da saye da sayarwa da takwarorinsu daga Najeriya.
Sakatare-Janar din kasuwar Gambari Ngara na Najeriya, Alhaji Bakari Balje, yace sun yanke shawarar sake bude iyakar ne saboda hare-haren ‘yan boko haram sun yi sauki kuma akwai bukatar cigaba da hada-hadar kasuwanci tsakanin Najeriya da Kamaru.
Mijinyawa Bakari, gwamnan jihar arewa mai nisa, ya ce matsanancin talauci da kuncin rayuwa a yankin da mafi akansin jama’ar ‘yan kasuwa ne da manoma, zai ragu. Amma yace za a asa ido akan jama’a da sana'o'insu.