Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Damke Wani Fitaccen Dan Majalisar Wakilan Nijeriya Bisa Zargin Sama Da Fadi


Rantsar da sabuwar gwamnatin Nijeriya
Rantsar da sabuwar gwamnatin Nijeriya

Hukumar yaki da almundahana da dukiyar al’umma ta Nijeriya, ta damke wani babban dan Majalisar Dokokin kasar bisa zargin damfarar gwamnati na miliyoyin daloli.

Hukumar yaki da almundahana da dukiyar al’umma ta Nijeriya, ta damke wani babban dan Majalisar Dokokin kasar bisa zargin damfarar gwamnati na miliyoyin daloli.

Hukumomi sun ce sun kame Kakakin Majalisar Wakilai mai baring ado, Dimeji Bankole, bayan wata turjewa ta tsawon sa’a hudu a gidansa da ke Abuja da daren Lahadi.

Hukumar Yaki da yin zagon kasa wa tattalin arziki na kyautata zaton Bankole ya yi sama da fadi da a kalla dala miliyan 60 mallakin Majalisar.

Bankole ya gaya wa hukumar cewa zai gabatar da kansa don amsa tambayoyi ran Litini. To amman kakakin hukumar EFCC Femi Babafemi ya ce jami’an hukumar sun yanke shawarar daukar wannan matakin ne bayan da wasu bayanan sirri su ka nuna cewa tsohon Kakakin na shirin sulalewa daga kasar ran Lahadi.

Wani mai magana da yawun Bankole ya karyata zargin cewa Kakakin ya yi amfani da matsayinsa na kakakin Majalisa don amfanar kansa.

Bankole bai yi nasara ba a zaben watan Afirilu a yinkurinsa na sake cin zabe kuma ya kasance Kakakin Majalisar har zuwa ranar Jumma’ar da ta gabata, a lokacin da tsohuwar Majalisar ta yi zamanta na karshe.

XS
SM
MD
LG