Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Kawancen Kungiyoyin Siyasa Da Za Su Kalubalanci Manyan Jam’iyyu A Zaben Ghana


Taron Kawancen Kungiyoyin Siyasa Da Za Su Kalubalanci Manyan Jam’iyyu A Zaben Ghana
Taron Kawancen Kungiyoyin Siyasa Da Za Su Kalubalanci Manyan Jam’iyyu A Zaben Ghana

Kungiyoyin siyasa guda 9, a kasar Ghana, sun hada kawance don tsayawa takara a babban zaben kasa mai zuwa da za a gudanar a Disambar 2024.

ACCRA, GHANA - Kungiyoyin sun dauki wannan matakin ne da nufin karya lagon manyan jam'iyyun siyasar kasar na NPP da NDC da suke bayayyar mulki tun da aka dawo jamhuriya ta hudu a Ghana.

Sabuwar kawancen da aka yi wa lakabin Alliance for Revolutionary Change, a karkashin jagorancin tsohon Ministan Ciniki da Masana’antu kuma jigo a jam’iya mai mulki ta NPP, Mr. Alan Kyerenmanten, da tsohon dan takaran shugaban kasa na jam’iyar CPP kuma jagoran kungiyar NIM a yanzu, Dokta Abu Sakara Foster.

Sauran sun hada da UGM na Akwesi Addai, da Ghana Green Party, Third Force Movement (TFM); da Non-Aligned Voters Movement; Crusaders Against Corruption.

Da yake jawabi a wurin taron kaddamar da kawancen kungiyoyin siyasan, Mr. Alan Kyeremanten, yace, ‘Muhimmancin wannan taron na yau, ya ta’allaka ne kan yadda muke bullo da wani tsari da zai sake fasalta tsarin tafiyar da harkokin siyasa a kasarmu."

Mr. Kyerematen ya kara da cewa, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, zai mayar da hankali ne wajen magance matsalar talauci da kuma sake saita kasar kan sabuwar hanyar ci gaba mai dorewa.

Sai dai wannan kawancen bai tsonewa manyan jam’iyun siyasa biyu da suka yi kaka-gida a mulkin kasar ido ba, wato jam’iyar NPP mai ci da kuma babbar jam’iyar adawa ta NDC, kamar yadda jami’un sadarwar jam’iyun suka ce.

Alhaji Aminu Abu na Madina, jami’in sadarwa ne na jam’iyar NPP, yace, ‘ In dai ba jam’iyun NPP da NDC ba, babu wata jam’iya da za ta iya. An sha kafa jam’iya da ake cewa karfi na uku, third force; muna daukar tsarin Amurka ne (na jam’iyu biyu)’.

Adel Umar na jam’iyar NDC yace idan wata jam’iyar siyasa za ta rasa kuri’a sanadiyar wannan kawancen, to ba jam’iyarsa ta NDC ba, sai dai jam’iyar NPP domin jam’iyarsa ta NDC na da magoya baya masu tushe, ba kamar jam’iyar NPP da yake akwai tushen wasu masu goyon Mr. Alan Kyeremanten domin, ‘hasashen da ya fito na kwanan nan na nuni da cewa, karin kuri’un Alan ya hau kuma na Bawumia ya sauko. Hakan na nufin cewa a cikin jam’iyar NPP din, wasu za su jefawa Alan kuri’a’. Yace, amma, magoya bayan NDC ba za su yi hakan ba.

Fitaccen mai hasashen zabe, Mussa Dankwah, darektan gudanarwa kuma shugaban bincike na kamfanin InfoAnalytics yace idan wannan kawancen ya yi kokarin jawo wasu ‘yan NDC da kuma wadanda ba su goyon bayan kowace jam’iya a cikinsu, to za su iya juya zaben zuwa zagaye na biyu.

Ya ce, karfin kawancen na ga Alan Kyeremanten da Abu Sakara ne kawai, don haka, ‘sai sun yi kokarin jawo wasu ‘yan jam’iyar NDC a cikinsu da kuma wadanda ba su jam’iya. In sun yi hakan, zaben zai iya zuwa zagaye na biyu’. Bisa ga cewarshi, idan ba su yi hakan ba, ba za su yi tasiri a zaben ba.

Yanzu dai waɗannan ƙungiyoyin siyasan sun haɗa ƙarfi a ƙarƙashin jagorancin Alan kyerenmanten don baiwa 'yan Ghana karin zabi ga ‘yan takara da za su zaba a babban zaben 2024 da za a yi a watan Disamba mai zuwa.

Saurari cikakken rahoto dagha Idris Abdullah:

 An Kaddamar Da Kawancen Kungiyoyin Siyasa Da Za Su Kalubalanci Manyan Jam’iyyu A Zaben Ghana.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG