Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaiwa Kiristoci Hari Su Na Cikin Ibada A Jami'ar Bayero


Ana cire wata gawa daga mota a kofar Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano bayan harin da aka kaiwa Kiristoci su na cikin Ibada a jami'ar Bayero
Ana cire wata gawa daga mota a kofar Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano bayan harin da aka kaiwa Kiristoci su na cikin Ibada a jami'ar Bayero

Shaidu sun ce mutane 15 a kalla sun mutu wasu kuma da dama sun ji ciwo

Shaidu sun ce wani harin da aka kai cikin wani babban dakin karatun Jami’ar Bayero ta Kano, wanda Kiristoci ke yin Ibada a ciki, ya halaka mutum 15 a kalla.

Haka kuma akwai labarin cewa dimbin mutane sun jin ciwo, amma ba a tabbatar da kamalallen adadin su ba.

Shaidu sun ce maharan sun je jami’ar ta Bayero ce a kan babur da kuma mota, su kai ta jefa boma-bomai tare da yin harbi.

Nan take babu wanda ya fito fili ya dauki alhakin kai harin, amma a can baya kungiyar Boko Haram ta masu tsattsauran ra'ayin addini ta sha kai hare-hare kan Kiristocin Najeriya.

Kirsimetin da ya gabata ma wasu fashe-fashen boma-bomai a wurare hudu daban-daban a kalla sun halaka mutane 39, da su ka hada da wasu masu dimbin yawa a Majami'ar Katolika da ke kusa da Abuja, kuma kungiyar Boko Haram mai haramta ilimin zamani salon na kasashen Turawa, ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare.

Kungiyar ta ce so ta ke yi ta kafa wata kasar Islama a arewacin Najeriya kuma ta ce ba ruwan ta da gwamnatin kasar, sannan kuma ba ta bin kundin tsarin mulkin kasar.

Wasu daruruwan mutanen sun mutu a bara cikin hare-haren boma-bomai da harbe-harben da aka dorawa Boko Haram.

XS
SM
MD
LG