Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Mace A Matsayin Ministan Tsaro A India


Buhari Ya A India
Buhari Ya A India

An nada mace a matsayin ministan tsaro a kasar India, Hakan ko ya biyo bayan garanbawul ne da Prime Ministan kasar Nerendra Modi yayi wa majilisar gudanarwansa.

Jiya Lahadi Firaministan Indiya Narendra Modi ya nada wata mace a matsayin Ministar Tsaro, bayan da ya yi garanbawul ma Majalisar Ministocinsa, a wani yinkuri na cike wasu muhimman alkawurra da ya yi tun kafin babban zabe da za a yi nan da shekara daya da rabi.

Nirmala Sitharaman za ta zama mace ta farko a wannan matsayin tun bayan shekaru 35, lokacin da tsohuwar Firaministar Indiya Indira Ghandi ta zama Ministar Ma'aikatar ta tsaro ita ma.

Sitharaman, 'yar shekaru 58 da haihuwa kuma tsohuwar karamar Minista a Ma'aikatar Kudi, ta hau wannan mukamin ne a daidai lokacin da takaddama tsakanin Indiya da makwabtanta biyu da ke sashin arewa, wato China da Pakistan ke dada tsanani. Ana yaba mata saboda karfin hali da kwarewa da kuma hazaka.

Ita ce mace ta biyu kan babban mukami a Majalisar Ministocin, Sushma Swaraj ita ce Ministar Harkokin Wajen kasar.

Modi ya nada sabbin ministoci 9 a yayin da ya ke mai da hankali kan gudanar da shugabanci na gari a tsawon shekara daya da rabi da ya rage a wa'adinsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG